Iyalan Wani Masanin Kano da Aka Sace sun shiga Damuwa bayan waadin da masu garkuwa da mutane suka debar musu.

Iyalan wani fitaccen malamin addinin musulunci na Kano, Sheikh Abdullahi Shehu Mai’Annabi, wanda aka yi garkuwa da shi tare da kaninsa da kuma dalibansa 11 da ke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Zamfara, kwanaki 40 da suka gabata, suna cikin fargaba saboda wa’adin da masu garkuwar suka bayar na biyan kudin fansa ya kare.

Masu garkuwan sun bai wa iyalan 12 ga Afrilu – 20, 2021 su tara N5m don daidaita kudin fansa na N10m da suka nema su saki mutane tara da ke hannun masu garkuwar.

An rawaito yadda aka umarci dangin su dauki gawarwakin mutane hudu daga cikin wadanda aka yi garkuwa dasu bayan sun biya Naira miliyan 5 ga masu satar mutanen.

Babban dan malamin, Malam Isyaku, da kyar ya iya rike hawayensa yayin da yake ba da labarin halin da iyalin suka shiga tun lokacin da aka sace mahaifinsa a watan Maris.

Ya ce sakamakon haka, matan mahaifinsa uku sun bar gidajen aurensu yayin da dangin ke kokarin tara kudi don ganin an sako malamin da aka sace tare da dalibansa.

Ya ce masu satar mutanen sun kira dangin a ranar Litinin, suna barazanar cewa za su kashe wadanda suka kama idan dangin suka gaza biya musu bukata zuwa ranar Talata, 20 ga Afrilu.

“Sun ce idan ba mu tara kudin ba kafin ranar da za a fada za su kira mu mu dauki gawarwakin wadanda aka sace.”

Ya ce masu garkuwar sun ba mahaifinsa damar yin magana da shi don shawo kansa cewa yana raye.

“Amma ba mu da abin da za mu sayar don samun kuɗin. Ko da N5m na farko da muka fitar a baya ya tashi ne daga iyayen Almajirai da aka sace kuma a wannan lokacin ba mu san inda zamu je don a taimaka mana ” a cewar sa yana kuka.

Malamin wanda ke zaune a Rimin Kebe tare da mambobin tawagarsa 12, ciki har da ’yan’uwansa da dalibansa, an sace su ne a ranar 8 ga Maris, 2021 a kusa da garin Sheme na Jihar Katsina da wasu‘ yan bindiga suka yi.

Da farko masu garkuwan sun nemi a ba su Naira miliyan 15 amma daga baya suka daidaita kan Naira miliyan 10.

Da aka tambaye shi ko sun tuntubi ‘yan sanda kan batun satar da kisan, Isyaku ya ce a Katsina aka sace mutanen kuma an tattara gawarwakin mutanen hudu a garin Kuyallo na jihar Kaduna.

“Mun kasance a rundunar‘ yan sanda ta Kano tare da mahaifiyata don gabatar da korafin ga kwamishinan ‘yan sanda na jihar. Mun jira na tsawon awanni amma ba mu samu ganinsa ba kuma hakan ya kashi mana karfin gwiwa da kuma rungumar kaddara, ”Isyaku ya kara da cewa.

Lokacin da wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce rundunar ba ta da masaniya game da lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *