Jami’an ƴan sanda ne kaɗai za su iya kawo ƙarshen ta’addanci a Najeriya-A cewar tsohon wani Sufetan ƴan sanda

Tsohon Sufetan ƴan Sanda Ya Bayyana Hanyar Da Gwamnati Zata Bi Ta Magance Matsalar Tsaro

Wani tsohon sufetan ƴan sandan ƙasar nan ya baiwa gwamnatin tarayya shawarar yadda zata yi ta daƙile matsalar tsaron ƙasar nan da jami’an ƴan sanda kawai – Ya ce babu isassun ƴan sanda a ƙasar nan idan ka kwatanta da yawan jama’ar da Najeriya ke dasu – A cewar tsohon Sufetan idan har gwamnati ta ɗauki sababbin jami’an ƴan sanda, sannan kuma ta kula da walwalarsu yadda yakamata to zasu iya magance matsalar tsaro gaba ɗaya. Tsohon sufetan ƴan sandan ƙasar nan Ibrahim Kpotun Idris ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta ɗauki sabbin jami’an yan sanda matuƙar tana son ta kawo ƙarshen ƙalubalen tsaron da yaƙi ci yaƙi cinyewa. Idris yace dalilin da yasa matsalar tsaro take cigaba da ruruwa a ƙasar nan shine saboda rashin isassun jami’an yan sanda da kuma rashin kula da su yadda yakamata. Tsohon sufetan wanda ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, yace idan ka kwatanta adadin yan sanda da yawan al’ummar Najeriya, zaka tabbatar da babu isassun jami’an yan sanda. Tsohon Sufetan Yan Sanda Idris yace:

” Babbar matsalar ita ce babu isassun yan sanda, jami’an na aiki ne a wahalce idan ka haɗa da yawan al’ummar da muke da su a Najeriya”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *