Rahotanni sun tabbatarda mutuwar shahararren kuma ɗaya daga cikin Shuwagabannin ƴan Bindiga mai suna Alhaji Karki a Jihar Neja.
Alhaji Karki ya kasance ɗaya daga cikin futattun ƴan Bindiga da suka addabi al’umma a Jihar Neja.
Akwai ɗaruruwan yara waɗanda suke ta’addanci a ƙarƙashinsa.
Tsohon mai magana da yawun Sojojin Nigeria, Sani Usman shine ya wallafa game da mutuwar wannan ɗan ta’adda. Wanda aka tabbatarda Jami’an tsaron Nigeria ne suka kashe shi.
Rahoto | Ya’u Sule Tariwa