Jami’an Yan sanda sunyi alkawarin taimkawa jami’an EFCC wurin kawo karshen cin hanci da rashawa. 

Yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria ta kamo wata sabuwar hanya a yayin da jami’an EFCC, jami’an DSS da kuma jami’in yan Sanda na Nijeriya sukayi alkawari wurin hada gwiwa domin kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar.

An bayyana haka ne a yayin da shuwagabannin EFCC na sashen ofishin Kaduna da Ilorin suka kai ziyara zuwa ga wasu wurare na takwaran ayyukansu na jami’in tsaro.

Wannan ziyarar an kaiwa darakta ne na DSS da kwamishinan yan sanda na garuruwan guda biyu.
Shuwagabannin EFCC din sun yabawa jami’an tsaro na DSS da yan sanda akan goyon bayan da suka bada wurin yaki da cin hanci da rashawa musamman ma a wasu manyan bangarorin.

Wadan nan manyan bangarori sun hada bibiya da kama masu laifukan safarar kudin haramun (money laudering) da kuma masu tallafawa ta’addanci.

Sannan kuma sunyi kira da su kara karfin gwiwa wurin hadin kai tsakanin jami’an EFCC da jami’an yan sanda wurin yaki da cin hanci da rashawa.

Gami da hakan, Kwamishinan yan Sanda na kwara Muhammad Bagega yayi alkawarin bama jami’an nan masu yaki da cin hanci da rashawa goyon baya a kowane lokaci.

Ya fadi cewa tinda hukumomin kamar yan uwan juna ne, duk wani taimako da ake bukata za’a samar da shi, na yaki da kuma fasaha.

Yace, “Zamu baku goyon baya akan kokarin ku na kawo karshen cin hanci da rashawa”.

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *