Jam’iyyar APC ta baiwa ƴan Najeriya tabbacin gwamnatin Buhari zata cigaba da basu kariya

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, ta baiwa ƴan Najeriya tabbacin cewa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, za ta ci gaba da amfani da dukkan matakan da suka dace wajen tabbatar ganin ta baiwa jama’a kariya.
Sakataren kwamitin rikon kwarya na kasa na jam’iyyar John Akpanudoedehe, shi ne ya ba da wannan tabbaci, cikin wata sanarwar da jam’iyyar ta fitar game da matsalar tsaro dake addabar sassan kasar. Yana mai cewa, jam’iyyar APC ba za ta sanya batun siyasa a batutuwan da suka shafi rayuka da jin dadin ƴan Najeriya ba.
Ya ce jama’a na kokawa game da matsalar tsaro, kamar ayyukan Boko Haram, da ƴan bindiga da masu satar mutane, da satar dabbobi, sai na baya-bayan nan hare-hare da ake kaiwa ofisoshin jami’an tsaro a wasu jihohin kasar.
A cewarsa, wadannan su ne abubuwan dake faruwa a halin yanzu a kasar, yana mai jaddada cewa, jam’iyyar APC tana mayar da hankali tare da gano dama hukunta masu aikata wadannan munanan ayyuka da masu daukar nauyin haddasa matsalar tsaro a kasar.

Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *