Katsina: ‘Yan kudu mazauna Arewa sun koka saboda barazanar Matawalle ta cewar za’a kai musu harin ɗaukar fansa.

Tashar mota tana cika da matafiya masu hijira

Barazanar tana zuwa ne daga wasu daga cikin shugabannin Arewa a farkon wannan satin, mutanen arewa zasu soma maida martani dai-dai da yadda akeyi wa ‘ƴan Arewa dake zaune a kudu, wanda tuni dai wannan kalamai suka ƙaɗa hantar ‘ƴan kudun dake zaune a jihar Katsina, dama wasu sassa na ƙasar.
Wata majiya ta bayyanawa jaridar Dailypost cewar, wannan ƙalubalen tuni ya jefa tsoro da fargaba na tunanin cewa mafusatan jama’a daga yankin ka iya kawo ma ‘ƴan kudu hari ko wani lokaci.

Shidai Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya tauna tsakuwa ne domin aya taji tsoro ta hanyar wata takarda daya sawa hannu a ranar Alhamis din data gataba, gwamnan ya gargaɗi ‘ƴan kudu cewar, Arewa a shirye take ta soma ɗaukar fansa akan yan Kudu dake zaune a Arewa. A cewar gwamnan:

“Babu wani yanki ko al’umma da bata iya tada zaune tsaye ba”
“Arewa ita ma ba kanwar lasa bace wajen nuna ƙeta da ƙyama,” Inji Gwamnan.

Matafiya nata hada hada

Bugu da ƙari, wani ɗan majalisar dattawa mai ci yanzu, Sanata Ahmad Baba Kaita, wanda yake wakiltar Katsina ta Arewa ya saki wani ƙwarya ƙwaryan rubutu mai taken “Arewa: Lokacin da haƙuri gamida shiru shiru bai zama zaɓi ba”, inda yayi gargaɗi game da haɗarin da ke zuwa ga ‘yan kudu da ke zaune a Arewa.

“Yayin da yakasance tafki ya dena ƙaɗawa, hakan baya nufin a cikin tafkin babu kada. Zage zagen da ake mana, munyi shiru acikin daraja da lalama, ba yana nufin bamu da salon maida martani bane ko bamu san inda ake taka wasan bane,” Inji Sanata Kaita.

Wannan kira da jigogi a Arewa sukayi, yasa Jaridar Dailypost ta samu sahihan hujjoji dake nuni da cewa, tuni matafiya suka dinga amsar kiranye kiranye daga yan uwansu da masu fatan alkairi da suke zaune a Arewa, kafin abin ƙi ya faru.

Wata budurwa dakeyin bautar ƙasa a Arewa, kuma bata koma kudu ba tun bayan kammala karatun nata, tace: “Kafin wannan lokacin, saboda yawan sace sacen mutane da yan ta’adda keyi, yan uwana sunyi ta faman takuramin akan na koma Kudu, amma naƙi. Amma da wannan barazanar daga babban mutum kamar gwamna, tabbas babu wani sauran dama daya rage mun, face na tattara komatsai na , na koma Kudu.”

Haka ma wani ɗan Kudu yace “Daga ƙarshe dai, lokacin bari na Arewa yazo. Ƴan Arewar dana sani basa yin wasa idan suka fara abu, suna yinsa ne bil haƙƙi.”

Ɗan kudun, yayi nuni da yadda garkuwa da mutane ya zama gama gari a yankin. Inda ya ƙara da cewa:
“Lokacin da garkuwa da mutane ya soma bunƙasa a arewa, gabaki daya ita kanta mummunar al’adar ta sauya salo.
“Yanzu babu wanda ya tsira.
“Garkuwa da mutane a arewa basai masu kuɗi ba kawai, harda talakawa ma ƙwamushewa akeyi.

“Duk da haka, bazan bar Arewa ba, idan zasu kashe ni, su kashe ni, amma tabbas zan tura iyalai na gida nan bada jimawa ba, da zarar an bada hutun ƙarshen zango. Mutum baya wuce lokacin da aka tsara masa zaiyi a duniya,” Inji wani ɗan Kudu.

Har cikin raina ni yanzu Arewa gida ce gareni, domin nan ne wajen zaman mu, kuma anan muke samun nakaiwa bakin salati. Idan ka ganni a kudu, naje ne kawai domin wani biki ko kuma zuwan ya zama dole. Amma idan suka ce zasu kashe mu, bamu da zaɓi face mu fece. Muna buƙatar gwamnati ta samo maslaha akan wannan barazanar da muke fuskanta, saboda mu dawo cikin walhala kamar da, tare da rayuwa a duk inda muke so a matsayin mu na ‘yan ƙasa ɗaya al’umma ɗaya. Inji wani ɗan Kudu.

A wannan ƙadamin da ake ciki, wasu sanannun muryoyi dake amo a ƙasar nan, sun yi watsi da wannan barazanar da Gwamnan yayi.
Ga kaɗan daga ciki:

“Ba adalci bane ace wai don ana kashe yan arewa a kudu, muma zamu kashe yan Kudu a namu yankin ba. Hakan ba dai dai bane, kuma Kungiyar Tuntuba ta Arewa na Allah wadai da wannan batu. yin hakan shine hanya mafi sauƙi wajen wargaza ko wacce ƙasa yayin da kowani ɗan ƙasa ya kasance zai ɗauki doka a hannunsa ta hanyar ɗaukan fansa,” saboda haka, bama tare da wannan ra’ayi,” Inji ƙungiyar tuntuɓa ta arewa.

“Bama yin farin ciki da wannan sanarwar ta gwamnan. Bayani irin wannan bai dace ace yazo daga shugaba ba, wanda yake riƙe da muƙami babba kamar na gwamna ba,”
In ji Shugaban Majalisar Yarbawa ta Oba Oba da Sarakuna a Arewacin Najeriya, Alhaji Mohammed Arigbabuwo.

“Mun tabbatar da cewa, shi (Matawalle) kawai yanayin ƙoƙarine ya samu sahalewar jam’iyyar sa ta APC domin ya samu cin nasara a zaɓen da zai shiga na gwamna zagaye na biyu.
“Abin kuma ya bamu kunya sosai akan yadda yayi maganar matuƙa. Matsalar daya dace mu fuskanta shine matsalar makiyaya da manoma ta rikici,” Inji Mai magana da yawun haɗaɗɗiyar kungiyar inyamurai ta ƙasa, wato Ohanaeze Ndigbo, Alez Ogbonnia.

Amma fa duk da haka, mazauna kudu basa ɗaukar gargaɗin Matawallen da wasa, saboda tuni wasu daga cikin su suka soma neman mafita mai ɓullewa daga wannan yanayi maras tabbas.

Babban dalilin da yasa ake ganin Gwamna Matawalle yayi wannan zafafan kalaman, baya rasa nasaba da irin rikicin kabilanci daya faru a “Rikicin Kasuwar Sasha” a watan Fabrairu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *