Tsaro

Ko Dokar Kasa ta bawa Shugaban Kasa damar kaima Kasar UKRAINE dauki ?

Spread the love

Kamar yadda muka sani Nigeria kasa ce babba da ke da fadin Murabba’i 923,768, kana kuma take da yawan Jama’a da suka kai kimanin Miliyan Dari 2, da 12.

A bangaren karfin tattalin arziki kuma ita ne ta 27 a duniya a Shekarar 2021, Kana kuma ta daya a Africa.

Haka ma a karfin Soji ba’a bar mu a baya ba, domin kuwa kasashen duniya da dama sukan turo manyan Sojojin su domin samun kwarewa da gogewar aiki a wurin Sojojin mu na Nigeria.

Sannan Kuma kowa ya san irin rawar da Nigeria ta taka a can Kasar Liberia da Gambia, da Guinue Bissau da kuma Kasar Sirri-leon lokacin da kowacce daga cikin wadannan kasashe suke cikin halin yaki, Nigeria ta tura dakarun ta sunje sun wanzar da zaman lafiyar da aka Dade ana nema a kasashen saboda karfin Soji da take dashi (Peace-Keeping Restoration), Don haka ne ma Nigeria ke amsa sunan “GIWAR AFRICA”.

Toh, anan ko Shugaban Kasa yana da damar da zai taimaka wa Kasar UKRAINE a Wannan yaki da ta tsinci kanta a ciki ?

Abin da ya kamata mu fara sani Shine, Shi irin Wannan taimako idan Mun Koma Dokokin Kasa-da-Kasa (International Law) zamuga cewa akan yi shi ne idan ya zama kasashen dake yakin daya mai karfi ce daya kuma marar karfi, to Kuma sai mai karfin ta ci gaba da Cin zalin marar karfin, to sai a hadu a taimaki ita marar karfin da ake Cin zalin ta, ko kuma idan ya zama dayan kasar da take yakin tana cikin kungiyar NATO, to su mambobin kungiyar za su taya ta Wannan yakin.

Sannan idan ya zama akwai kawance (Friendship) tsakanin Kasashe biyu to idan daya tana cikin halin yaki dayar za ta iya kawo mata agaji (Kamar yadda ake tsoron kar Kasar China ta Kawo ma Kasar Rasha agaji, domin kuwa Kawar ta ce, idan China ta kawo mata dauki to ita ma Kasar ta Ukraine Kasashen da suke kawance da ita zasu kawo mata agaji ita ma, to idan hakan ta faru zai iya haifar da yakin duniya na Uku, domin kuwa ko yakin duniya da akayi na daya da na biyu kusan daga haka aka fara).

Saboda haka Wannan Kawancen zai iya hana Kasar Nigeria taimakawa Kasar Ukraine, domin kuwa a Shekarar 2019 Nigeria ta Kulla yarjejeniyar Karfin Soji da Kasar ta Rasha, dan haka sun zama Kawaye, babu maganar taimakawa Kasar Ukraine, saidai ma idan al’amura suka rincabe (bama fata) Nijeriyar ta taimakawa Kasar ta Rasha da Dakarun ta, duk da daman, akwai wasu kalamai na Shugaban kasar Rasha din, inda ya gargadi Duniya akan cewa kar kasar da ta sake ta tsoma masu baki ko tayi masu katsalandan a Wannan yakin, duk wacce ta kuskura tayi to lallai kuwa za ta dandana kudar ta.

To, amma duk da haka, Shugaban Kasar mu Na Nigeria, yana da hurumin da zai kaima Kasar ta UKRAINE agaji bisa Cin zali da ake ganin Kasar Rasha tana yimata saboda ta ga ta fita karfi, ta hanyar turawa da dakarun shi da tankokin yakin shi kai har da makamai masu linzami zuwa kasar ta Ukraine dan bata agajin gaugawa.

Mu duba Kundin tsarin Mulkin Nigeria Sakin layi Na 5, Sashi Na 5, Babi Na Daya, zamuga ya bawa Shugaban Kasa damar turawa da dakarun shi zuwa wasu kasashen don taimaka masu wajen tabbatar da tsaron kasar su, ko wanzar da zaman lafiya, amma fa dole sai ya samu sahalewar ‘Yan Majalisun shi (Senators da House of reps) Kuma dokar batace wai iya Africa bane Kawai Shugaban Kasa yake da hurumin tura Dakarun shi ba, a’a duk duniya ne (Wato kowace Kasa ce a duniya) kamar yadda yazo a cikin littafin “The Foreign Relations Powers of the Nigerian National Assembly” na Barr. J. O. Arowosegbe da Barr. R. J. Akomolafe.
NB:

Amma kawancen da ke tsakanin Kasashen biyu zai hana Nigeria taimakawa Kasar Ukraine inma ta kama saidai mu taimakawa Kasar ta Rasha.

Shehu Rahinat Na’Allah
25th February, 2021.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button