Ko kadan Burutai bai yi adalci ba, bai kamata ya zargi Sojoji ba, in ji Sanata Ali Ndume.

Sanata Ali Ndume ya mayarwa da shugaban sojojin Najeriya Tukur Yusuf Burutai martani.

Da yake bayani yau a Abuja, sanata Ali Ndume ya ce Sam Sam shugaban sojojin Najeriya Tukur Yusuf brutai bai yiwa ‘yan’uwansa sojoji adalci ba bisa zargin su da hada baki da wasu manyan yan siyasar kasar nan wajen shirya juyin mulki a karkashin kasa.

Sanata Ali Ndume ya ce Tukur Yusuf Burutai yayi amfani da wannan furucin da ya yi ne kawai don ya wanke kansa da gazawar da suka nuna wajen rashin iya tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Najeriya musamman arewa maso gabashin kasar.

Ali Ndume yace halin da ake ciki yau a Najeriya duk Duniya ta tabbatar da irin gazawar da shugabannin tsaron kasar nan sukayi Na rashin iya kawo karshen ta’addaci kamar yadda jam’iyarsu ta APC tayi alkawari.

A wasu ‘yan lokatai da suka wuce shi shugaban sojojin Najeriya Tukur Yusuf Burutai ya sha fitowa yace sun murkushe ‘yan kungiyar boko haram a Najeriya Wanda mu da ta’addancin yafi shafar bangaren mu muna jinsa munsan ba haka bane amma bamu taba fitowa mun karyata shi ba.

Sanata Ali Ndume yace yana kira ga shugaban sojojin Najeriya Tukur Yusuf Burutai da ya janye wancan kalamai nasa Na zargin wasu sojojin Najeriya da hada baki da wasu ‘yan siyasar kasar nan da yunkurin shirya juyin mulki a boye, domin shi kansa ya san wannan lafazin nasa ba gaskiya bane yayi ne kawai don ya wanke kansa da kuma yaudarar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari don karya kai ga fahimtar cewa sun Gaza ya canza su da wasu, inji Sanata Ali Ndume.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published.