Ku daina ƙoƙarin kaini bango, zan iya sheƙe ku duka – Buhari ya faɗawa ƴan fashi da masu garkuwa da mutane.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da kisan mutane goma da ƴan bindiga sukayi a Jihar Zamfara.

Shugaban, ya gargaɗi yan fashin da cewa “Wannan dabi’a tasu ta rashin daraja rai, zai kawo karshen sa da gaggawa”.

Shugaban yayi wannan iƙirarin ne yayin da yake jajantawa waɗanda abin ya shafa inda yace kisan da ake yiwa mutanen da basu ji ba, basu gani ba dole ne ya tsaya.

Ya ƙara da cewa: “Waɗannan mugaye, dole ne su daina ƙoƙarin gwada sa’ar su abisa tunanin cewa mun gaza, ko kuma bamu da yadda zamuyi na ganin mun murƙushe su”.

Shugaban ƙasan ya umarci jami’an tsaro da tattara bayanan sirri kuma su ɗauki matakin gaggawa wajen warware duk wani lam’a da ake samu wajen ɓarakar data dabaibaye aikace aikace na tsaro.

Shugaban ya nuna kyakkyawan fata cewar, Aiki na Musamman da sojoji suka rantsar a Ƙaramar hukumar Maru da misalin ƙarfe uku na dare zai kasance babban makami wajen samun nasara a ƙoƙarin kakkaɓe aikin ƴan ta’addan

“Bazamu lamunci yiwa talakawa rashin daraja ba, a kyale su suji da talauci da lalacewar tattalin arziki dayake damun su, sabanin kyale mutane su wataya, bazamu bari ba gaskiya,” ƙasa ya gargaɗe su.

Bugu da ƙari, Buhari yayi kira ga jami’an tsaron ƙasa da su ƙara ƙaimi wajen kawo

ƙarshen wannan rashin mutunci da ake wa mutanen basuji basu gani ba.

“Kada mu bawa waɗan nan miyagu damar samun nasara, ta
hanyar ɗaukar makamai da muke dasu zuwa yankinsu, idan mukai haka zamu samu damar tsayar dasu tun kafin su samu damar maida martani na luguden narkon ruwan wutar mu”.Buhari ya ƙara tabbatarwa mutanen jihar Zamfara cewar “Duk da koma bayan da muka samu wajen kare dukiyoyinku da rayuwanku, daga yanzu babu ɗaga ƙafa a ƙoƙarin da muke ba ganin mun murƙushe abokanan gabar ganin tabbatuwa ta al’umma”.

Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *