Masu ƙwacen wayar salula sun karya azumin su a Kano

DSP AH kiyawa shine mai magana da yawun hukumar ƴan sanda ta jihar Kano, kamar yadda ya bayyana a wani holin masu laifi daya gabatar, ya zayyana cewa:

Abisa umarni daya samu daga Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano CP. Sama’ila Dikko (Nagari na kowa) biyo bayan ƙorafi da ƴan sandan Jihar Kano suka samu na ƙorafe ƙorafen al’umma na cewar ana yi musu sanen wayoyi, yasa hukumar ƴan sandan basuyi ƙasa a gwuiwa ba suka tashi yan sanda nan na kan kace kwabo.

Inda suka bazama kuma cikin ikon Allah suka samu nasarar kama wasu matasa guda biyu masu tuka adaidaita sahu da suke kitsa laifin kwacen wayar salula ta hanyar sane.

A cikin masu laifin akwai Usman M. Usman mai shekara 20, wanda shine ke tuƙa adaidaita sahun, kuma yake kallon yanayin motsin wanda za’a ɗaukarwa abu ta madubi, kuma yake taka burki idan an saka waya a gaban aljihu domin ta faɗo.

Sai kuma wanda yake zama a wajen pasinja, mai suna Muhammad Ali daga Damaturun Yobe, wanda kwanan sa ɗaya da zuwa garin Kano, ya biyo Usman M. Usman domin yin wannan haramtacciyar sana’a tasu.

Usman dai da Muhammad Ali sun haɗu ne a makarantar kwana da suka yi a can Yobe mai suna Suleiman Idris.

A cewar Muhammad Ali, aikinsa idan an fita shine, lallaɓawa yayin da aka taka burki da ƙarfi, sai shi kuma ya lallaɓa yasa hannu a cikin aljihun pasinjan da tsautsayi ya afkawa. Idan kuma ta faɗo ƙasa, sai yace zai sauka , ya tafi da ita. In kuwa kagani, sai su baka abinka.

Duk da wannan aikata laifi da sukeyi na ta’asa, hakan bai hanasu ƙara wani tafka wani saɓon ba, domin kuwa, masu sanen wayar sun zayyana cewa, sufa basa yin azumi ma ɗungurungum a ranar da za’a kama su saboda sun san cewa, aikin haram zasu fita. a cewarsa:

“Saboda mun san za mu fita aikin Haram shi ya sa muka ajiye azuminmu”

Saida muka sha ƙwaya da safiya, kimanin ƙarfe 9 na safe”. Inji Usman M. Usman

Wani abin tashin hankali kuma, daga safiya kawai waɗannan matasa sun ƙwace wa mutane 6 wayoyin salularsu, inda ace kuma zasu wuni suna yi, wani irin ta’asa zasuyi ga al’ummar da basuji basu gani ba?

A tare dasu kuma an kama su da ƙudi, ƙwayoyin bugarwa, kayan sawa cike da jaka domin canjawa da dai sauransu.

Bisa umarnin Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano CP Sama’ila Dikko, yasa an maida waɗannan masu laifi sashin manyan laifuka dake Bompai. Kuma da zarar an kammala bincike za’a gurfanar dasu a gaban kotu, domin girban abinda suka shuka.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *