Matsalar Tsaro:- Gwamnan Jahar Neja Ya Gana da Gwamandojin Tsaron Jahar.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Gwamnan Jahar Neja kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa ta tsakiya Gwamna Abubakar Sani Bello Lolo ya Tabbatar wa Da Al’ummar Jahar cewa Ayyukan Ta’addanci ya kusa zama Tarihi a Jahar.

Gwamnan yace Akwai Sabon tsari da Jami’an Tsaro zasu dauko domin dakile Ayyukan Ta’addanci a Jahar.

Har Ila yau yace Mutane su Rika taimakawa Jami’an Tsaro da Bayanai kan Yan Ta’adda Domin Abin yazama Tarihi a Jahar.

Gwamnan Ya nuna matukar damuwarsa a kan Irin Kashe Kashen da Yan Ta’addan keyi a Wasu Sassan Jahar.

Gwamnan yayi wa Yan Jarida bayanin hakan ne Bayan Ya Gana da Kwamandojin Tsaro a Fadar Gwamnatin Jahar dake Minna.

Ko A Ranar Galata da tagabata wasu matasa Sun Gudanarda Zanga Zangar Lumana a Gidan Sarkin Minna kan Matsalar Tsaro da ta Addabi Kanan Hukumomin Shiroro, Magama,Munya da Rafi dake Jahar.

Muna Fatan Allah ya kawo mana Zaman Lafiya a Kasar Mu Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published.