
Muna aiki tukuru don ganin tsaro ya inganta a kowane bangare na Najeriya ba da jimawa ba.
Muna yin iya kokarinmu, muna saka kudi sosai wajen samo kayan aikin zamani.
Wasu sun iso, wasu kuma suna tashar Jiragen ruwa, kuma muna da wasu kuma suna kan hanyarsu.
Kalaman shugaban kasa Muhammadu Buhari Kenan wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Sai dai kuma Mutane da yawa sunyi tsokaci akan sakon, yayin da wasu suke kushewa wasu ko suna son barka.
Daga Sabiu Danmudi Alkanawi.