Tsaro

Mutane da yawa sun mutu yayin da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai hari a gonaki a Enugu.

Spread the love

Akalla mutane shida ne ake zargin an kashe bayan wani hari da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai a kauyukan Mgbuji da Ebo a Eha-Amufu, karamar hukumar Isi-Uzo ta jihar Enugu a ranar Alhamis.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa an fara kai harin ne da misalin karfe 10 na safe kuma ya kai har karfe 6 na yamma.

A cewar wani jami’in tsaron yankin da ya nemi a sakaya sunansa, akwai yiyuwar adadin wadanda suka mutu ya karu yayin da wasu manoman da suka samu raunukan harbin bindiga suka afka cikin dazuzzukan da ke kewaye, kuma har yanzu ba a kai ga ceto su ba.

Wata majiya wacce kuma ta nemi a sakaya sunanta ta ce adadin wadanda suka mutu ya kai 12, inda ya kara da cewa mazauna garin na ci gaba da neman ‘yan uwansu da suka bata.

Majiyar ta kuma ce, harin ya jefa al’ummar da suka fi yawan noma cikin alhini biyo bayan asarar ‘yan uwansu, inda ta kara da cewa mazauna yankin sun kaurace wa jama’a saboda fargabar sake kai hari.

An tattaro cewa rikicin ya fara ne a lokacin da wasu matasa suka fatattaki wasu makiyaya daga gonakinsu bisa zargin sun bar shanunsu sun lalata gonakin rogo mai hekta.

A fafatawar da aka yi tsakanin matasan da makiyayan, an ce an kashe wasu shanun, lamarin da ya sa makiyayan suka kaddamar da ramuwar gayya.

Ko da yake mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe, bai mayar da martani kan wannan lamarin ba, wani shugaban al’ummar Mgbuji, Eric Ebeh, ya tabbatar wa jaridar Vanguard harin.

Eric ya kuma ce har yanzu ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba yayin da al’ummomin da abin ya shafa ke ci gaba da sare ciyayi don samun karin wadanda abin ya shafa.

“Har ya zuwa yanzu, fargabar ba ta barin kowa ya shiga cikin gonakin don nemo wadanda abin ya shafa ko kuma tabbatar da irin barnar da aka yi ba. Ba ni a kauyen a halin yanzu amma na yi bincike kuma na tabbatar da cewa an kai hari kan al’ummata. Wasu daga cikin mutanen da na kira sun gabatar da alkaluma masu karo da juna. Yayin da wasu ke cewa an kashe mutane shida, wasu kuma sun ce adadin wadanda suka mutu ya kai bakwai ko takwas. Har yanzu ba mu san ainihin adadin wadanda harin ya rutsa da su ba,” inji shi.

Idan baku manta ba aƙalla mazauna wannan al’umma su uku ne suka rasa rayukansu a irin wannan hari a watan Janairun wannan shekara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button