Najeriya na fuskantar kalubalen tsaro na musamman ~ inji Amurka

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya bayyana kalubalen tsaro da ke fuskantar Najeriya a matsayin abin mamaki

Ya fadi haka ne a yayin wani taron tattaunawa tare da ‘yan jaridar Kenya da na Najeriya.

Blinken, wanda ke amsa tambayoyin kan yadda Amurka za ta taimaka wa Najeriya don tunkarar kalubalen tsaro da Boko Haram, barayi, da IPOB ke haifarwa.

Ya ce, “kalubalen da Najeriya ke fuskanta idan aka zo batun tsaro da ban mamaki – kuma kun kira su da da ta’addanci, da fashi, da miyagun laifuka ko kuma waɗannan duka ƙalubale ne na gaske.

“Na farko, muna bada cikakken hadin kai a tsakaninmu a kokarin magance wadannan kalubale tare.  Kuma Kasar Amurka ta himmatu wajen tallafawa Najeriya yayin da take fuskantar wadannan kalubalen.  Kuma wannan ya kunshi taimaka wa Nijeriya ci gaba da haɓaka ƙarfinta ta hanyar horo, ta hanyar albarkatu, ta hanyar musayar bayanai, ta hanyar kayan aiki.

“Amma kuma yana da mahimmanci mu yi aiki tare, kamar yadda muke, don magance abubuwan da suke janyo wannan lamari wanda muka san masu aikatawa suna ci a kai. Kuma wannan shine dalilin da ya sa dole ne ku sami cikakkiyar hanyar magance waɗannan abubuwa. 

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *