Najeriya ta fi tsaro a yau fiye da yadda take lokacin da muka karbi mulki – Garba

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya ce Najeriya ta fi tsaro a yau fiye da lokacin da shugaban sa, Muhammadu Buhari ya karbi mulki, yana mai cewa “Boko Haram yanzu ta na kan iyakar Tafkin Chadi” .

Ya yi magana ne yayin da akayi hira dashi a shirin ‘Siyasar Lahadi na Channels Television.

Da yake amsa tambaya, hadimin shugaban kasar ya ce, “Game da ta’addancin Boko Haram, Najeriya ta kasance kasa mai tsaro a yau fiye da yadda yake lokacin da muka karbi mulki.

“Sabon kalubale ya fito, rikicin manoma da makiyaya, kashe-kashe a sassan tsakiyar kasar, yawancin wadannan an shawo kan su. Matsalar zagon-kasa na shigarwar mai a Kudu-maso-Kudu an sarrafa shi har zuwa wannan lokaci.

“Kalubalen‘ yan fashi, sace-sacen mutane sun taso a sassan kasar da dama ciki har da Kudu maso Yamma. A yau, Kudu maso Yamma ita ce mafi tsaro a wannan ƙasar.

“Kalubalen na tattare da wasu sassan jihohin Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina da Kaduna. Yawancin shi (rashin tsaro) an kawar da shi a Kaduna. Katsina ta fi tsaro a yau fiye da shekaru biyu da suka wuce. Zamfara na fama da matsaloli – na asali.

“Maganar ita ce, matsalolin yayin da suke tasowa ana fuskantar su da kwararrun sojojin gomnati masu gaskiya, ‘yan sanda masu aminci da kuma hukumomin leken asiri wadanda suke da inganci.”

Daga Maryam Ango

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *