Ran maza ya baci Ministan tsaro yasha alwashin kawo karshen Ta’addancin Nageriya

Ministan tsaron Nageriya Bashir Magashi, ya sake nanata kudurinsa na sake fasali da tsarin tsaron kasar dan magance kalubalen tsaro da ake fama da shi. Mataimakin sa na musamman kan yada labarai, Mohammad Abdulkadri, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar din da ta gabata ya ce Magashi ya bayyana hakan ne yayin bikin baje kolin shekara wanda ya cika shekara daya a kan karagar mulki. Mista Magashi ya kuma bayyana kudurin gwamnati na ci gaba da wanzar da aikin gina sashin tsaro mai dorewa wanda zai tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsaro a kasar.

Ministan ya godewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa damar da ya bashi na yi wa al’umma aiki,

Leave a Reply

Your email address will not be published.