Rashin Tsaro: Ganduje ya yi fata fata da El-Rufa’i..

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya yi tir da kalaman da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yayi kwanan nan game da matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

Idan ba ku manta ba a baya-bayan nan ne El-Rufai ya bayyana a sashen Hausa na BBC cewa rashin hadin kai tsakanin gwamnonin Arewa maso Yamma na kawo cikas ga kokarin tsaro a yankin.

Duk da haka, da yake magana a Rediyon Faransa International, wanda a ranar Alhamis, Ganduje ya ce mai yiwuwa El-Rufai bai fahimci kokarin tsaro da gwamnonin yankin suke yi ba.

A cewar Ganduje, hukumomin tsaro a kasar sun shawarci Jihohin Kano, Kaduna da Bauchi da su hada kai su kuma duba kalubalen tsaro a sanannen dajin Falgore da ke cikin kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa na jihar Kano.

“Batun rashin hadin kai bai taso a wannan yanayin ba saboda hukumomin tsaro sun ba mu shawarar mu zo mu hadu da jihohin Kano, Kaduna da Bauchi don ganin yadda za a shawo kan ayyukan ‘yan fashi a dajin Falgore.

“Na yi kusanci da gwamnonin Kaduna da na Bauchi. Dukansu sun aika wakilansu.

“Akwai batun asusun. Kano, Kaduna da Bauchi duk sun ba da gudummawar kuɗaɗensu kuma aikin ya sami nasara.

”Yadda na ganta, Gwamna bai fahimci matsalolin tsaro sosai ba saboda yanayin tsaro ya dogara da yanayin jihar. Misali, duk yadda muke hada karfi da karfe a matsayinmu na gwamnoni, yaya ya kamata mu duba rikicin kabilanci a Kaduna? Ta yaya zamu bincika banbancin addini a Kaduna? Ka gani, wannan matsala ce wacce sai gwamnatin jihar Kaduna da kanta za ta iya dubawa.

“Saboda haka, duk wani batun tsaro a jiha ya dogara da kokarin gwamnatin jihar, da gwamnatin tarayya, da jami’an tsaro da kuma mutanen jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *