Rashin tsaro: Majalisar dattijai ta gayyaci Shugabannin rundunonin tsaro da shugabannin hukumomin tsaro su bayyana a gansu.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, a ranar Talata ya bayyana cewa shugabannin rundunonin tsaro da shugabannin hukumomin tsaro za su bayyana, a ranar Alhamis mai zuwa, a gaban majalisar.

Manufar kiran, kamar yadda Lawan ya ce shine yiwa majalisar dattijai bayani kan ƙoƙarin shawo kan matsalar rashin tsaro a ƙasar.

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Ezrel Tabiowo.

A cewarsa, bayyanar shugabannin hafsoshin zata kasance martani ne ga ƙudurin da majalisar dattijai ta yanke a makon da ya gabata, inda aka yanke shawarar cewa za a gayyaci shugabannin rundunonin da sauran shugabannin hukumomin tsaro kan matsalar rashin tsaro a jihohin tarayya.

Lawan ya bayyana cewa Shugabannin Ma’aikatan sun kasa amsa gayyatar gaggawa da aka yi musu tunda fari ne a yau saboda taron tsaro da ke gudana a fadar Shugaban ƙasa wanda aka tsara za a kammala a ranar Laraba ta wannan makon nan.

Ya ƙara nanata cewa saboda haka ne, yanzu shugabannin rundunonin za su bayyana gaban zauren majalisar a ranar Alhamis, 6 ga watan Mayu, na 2021.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *