Tsaro

Rikici a Zamfara: ‘Yan bindiga na neman Naira miliyan 60 a matsayin harajin zaman lafiya

Spread the love

Rahotanni sun ce an dora wa wasu al’ummomi a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara wani ‘haraji’ daban-daban.

Wani mazaunin Moriki da ke daya daga cikin al’ummomin karamar hukumar, Aliyu Buhari, ya ce ‘yan bindigar ta hanyar wadanda aka sako, sun bukaci a biya su kudaden harajin kafin a bar mazauna yankin su shiga gonakinsu.

Buhari ya ce wasu al’ummomi sun biya kuma sun amince da sulhu da ‘yan bindigar, inda ya kara da cewa a halin yanzu mazauna Moriki suna kokarin tara harajin.

“An bukaci mutanen da ke zaune a unguwar Moriki da su biya Naira miliyan 20 domin samun wani zaman lafiyan,” in ji shi.

A kwanakin baya an yi garkuwa da mutane biyu daga yankin Dauran kuma an biya kudin fansa domin a sake su, yayin da a garin Kanwa kuma aka yi garkuwa da mutane sama da 40 wadanda yawancinsu mata ne yayin da ‘yan ta’addan suka yi ta bincike gida-gida.

Har yanzu dai ‘yan bindigar ba su nemi kudin fansa ba domin a sako mutanen da aka sace.

A baya ‘yan fashin sun dorawa al’ummar Kanwa harajin m Naira miliyan 20. Wannan harajin na zama yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ‘yan ta’adda da al’umma.

Duk da biyan harajin, a halin yanzu mazauna yankin na cikin zaman dar-dar, saboda suna ganin cewa sace jama’a na baya-bayan nan na iya haifar da wani karin haraji.

Kowane gida zai ba da harajin N6,500

“A halin yanzu, mutanen yankin Moriki suna tunanin yadda za su ba da kuɗin. Kudaden da za a biya shi ne don a ba su damar shiga gonakinsu da zaman lafiya ba tare da fargabar kai hari ba,” inji Buhari.

Al’ummomi da dama sun riga sun biya kudin. Yawancinsu suna samun albarka a lokacin damina, lokacin da manoma ke buƙatar yin aikin gonakinsu.

“A Moriki, a lokacin damina, an bar mutane su yi noma, amma sun fara yi mana barazana a lokacin girbin amfanin gonakinmu.

“An bukaci kowane gida a Moriki da ya ba da gudummawar Naira 6,500 don cika harajin Naira miliyan 20.

“Na fahimci cewa wa’adin biyan kudin ya kasance a makon jiya Asabar, amma har yanzu al’umma na ci gaba da kokarin samo kudaden.

“Wasu al’ummomin da aka nemi su biya harajin sun hada da Gidan Shaho, Kadamutsa, da Dada.”

Suleiman Mahmud, wani mazaunin garin Zurmi, wanda shi ma ya yi magana game da ci gaban, ya ce an bukaci al’umma kusan 10 da su biya haraji na kudade daban-daban.

Ya kara da cewa wasu sun biya, wasu kuma har yanzu ba su samu kudin ba.

“A yankin Moriki, an nemi su biya Naira miliyan 20. Mazauna yankin sun kuduri aniyar biya, amma ban tabbata ko an kai wa ‘yan ta’addan ba.

“Suna sanar da jama’a duk wata al’ummar da suka kai hari game da bukatunsu. Suna sanar da wanda aka sako ko kuma su isar da saƙon a duk lokacin da suka kai hari ga al’umma.

“Tun lokacin da suka amince da biyan harajin sulhu a watan Yuli, ba su kai hari ga mutanen Moriki ba, kuma jama’a na ci gaba da gudanar da harkokinsu.”

A makon da ya gabata, an yi garkuwa da wasu mutane biyu daga gonakinsu, yayin da aka kashe mutum daya a kewayen yankin Dauran.

Wasu daga cikin al’ummomin da suka amince da yarjejeniyar zaman lafiya kuma suka biya kudin diyyar sun hada da Kwagwami, da Boko, da Jaya, da Dunfawa, da Gidan Goga.

Al’ummomin sun kai kusan 10 a karamar hukumar Zurmi. Kamar Kanwa, sun sanya Naira miliyan 20; Jaya, Naira miliyan 17; Moriki, Naira miliyan 20, yayin da Kwagwami, Naira miliyan 6.5.

Mahmud ya kuma ce an yi garkuwa da wasu mazauna garin Kwagwami kwanan nan, inda ya kara da cewa wadanda aka sacen na hannun su, sai hakimin da aka sako.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button