Sabbin hare hare da ‘yan bindiga suka kai a Sokoto sun tilastawa jama’a yin hijira daga garuruwansu.

Mazauna Bargaja, Tozai, Turba da Danzanke duk sun koma garin Isa sakamakon jerin hare-hare da aka kai wa garuruwansu.

Garuruwa da dama a jihar Sakkwato sun fice sun yi kaura sakamakon sabbin hare-haren da ‘yan bindiga suka kai, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane hudu.

Kwamishinan Tsaro na Jihar, Garba Moyi, wanda ya bayyana haka, ya ce ‘yan bindigar sun saci dabbobi a yayin harin.

A cewar kwamishinan, an kashe mutane uku a kauyen Bargaja da ke karamar hukumar Isa, yayin da aka kashe daya a cikin wata karamar hukuma a karamar hukumar Sabon Birni.

Jaridar DailyTrust ta rawaito cewa maharan sun mamaye Bargaja ne da misalin karfe 2 na ranar Alhamis, suna harbin kan mai uwa da wabi.

Wani mazaunin garin Isa, mai suna Surajo, ya ce mazauna Bargaja, Tozai, Turba da Danzanke duk sun koma garin Isa bayan wasu hare-hare da aka kaiwa kauyukansu.

“Ba sa kwana a wurarensu kuma. Wasu daga mazajensu ne da ke da filayen noma kusa da kauyen za su koma kowace safiya don yin aiki a kansu kuma su ruga zuwa garin Isa kafin faduwar rana, ”inji shi.

Wani mazaunin, mai suna Malam Sanusi, ya ce Gatawa a karamar hukumar Sabon Birni yanzu haka ya cika da ‘yan gudun hijira daga kauyukan da ke makwabtaka da shi.

A cewarsa, kauyukan sun hada da, Makera, Dankura, Burkusuma, Kumaro, Garin Tunkiya, Zangon Malam da Asha Banza.

Ya ce an kashe wani Malam Bilya Idris, wanda aka san shi da Idi Gago a kauyen Dankura, da kuma Malam Abdulmajid Abdurrahman, Muhammadu Hatimu da Yazzid Sa’idu sun rasa rayukansu a yayin harin na Zangon Malam wasu makonni da suka gabata.

Ya kara bayyana cewa yawancin mutanen da aka kashe ko dai kungiyar ‘yan banga ne ko kuma wadanda suka rasa dabbobinsu kuma suka yanke shawarar bin’ yan fashin.

“Wannan shine dalilin da ya sa ba ma karfafawa mutanen garin gwiwa su shiga cikinsu saboda muna da hanyoyinmu na dawo da duk abin da suka sata.

“Muna amfani da ‘yan uwansu wadanda suka rungumi zaman lafiya don kwato dabbobi har ma da makamansu tare da tabbatar da sakin wadanda aka sace,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *