Sakacin Gwamnonin Da Suka Gabata Ne Ya Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya, In ji Gwamna Badaru.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar ya bayyana cewa akwai laifi gwamnonin da suka gabata a matsalar tsaron da Najeriya ke fuskanta.

Gwamnan yace dalili kuwa shine basu samar da tsare-tsare masu kyau da zasu kyautata alaka tsakanin makiyaya da Manoma ba sannan babu tsari me kyau na kula da gandun daji.

Saidai gwamnan yace akwai gwamnoni 2 da suka gabata wanda sun yi kokari a wannan bangare, sune Saminu Turaki da Sule Lamido. Gwamnan ya bayyana hakane a yayin da ake kaddamar da shirin baiwa jama’a tallafi a kananan hukumomi 18 na jihar, kamar yanda aka samo muku daga TheNation.

Leave a Reply

Your email address will not be published.