Shekau ya saki bidiyo kan batun kwace gonarsa da ke dajin Sambisa.

Shugaban ‘yan boko haram Abubakar shekau ya fitar da wani sabon faifen odiyo, inda aka jiyo shi yana karyata wani faifen bidiyo da sojojin Najeriya suka saki, suna nuna cewa sun kwace Gonarsa a dajin Sambisa.

A cikin faifen odiyo din shugaban ‘yan boko haram Abubakar shekau yace shi kwata kwata ba shi da wata Gona a dajin Sambisa dama fadin Maiduguri gaba daya.

Abubakar shekau ya kara da cewa kuma harin da aka kai na cikin Birnin Maiduguri, yaransa ne sukayi harin bisa umarninsa.

Abubakar shekau ya ce kuma sun kai harin ne don su Dada tabbatar wa da sojojin Najeriya da kuma duniya cewa waccan jita jitar da sojojin suke yadawa duk karya ce, kuma su Dada nuna musu cewa suna nan kuma za su ci gaba da kai hare-hare ta kowanne hali.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *