Sojoji A Najeriya Sun Kashe ‘Yan Boko Haram Kuma Sun Ceto Mutane 7 A Borno.

Rundunar sojojin Najeriya a ranar Litinin ta ce sojojin Operation Lafiya Dole da ke yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabas sun kashe ‘yan ta’adda 9 a yayin wani aikin share-fage a karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno.

Kodinetan yada labarai na Operation Media Defense, Manjo Janar John Enenche, a cikin wata sanarwa ya ce yin aiki da sahihan bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ta’adda a garin Hamdaga Makaranta da ke Gwoza, sojojin runduna ta 192 da goyon bayan Sojojin Sama a Jiya lahadi 6 ga Satumbar 2020 sun mamaye wurin.

Ya ce, “Sojojin sun kuma gano wasu gine-ginen Boko Haram da ISWAP guda tara wadanda aka kebe da filayen noma a yankin.

“Bugu da kari, sun yi nasarar kubutar da mutane bakwai da aka sace wadanda suka hada da mata biyu da yara biyar.

“A yanzu haka gwanayen sojojin sun mamaye yankin da yawan sintiri Inji Shi.”

Enenche ya ce babban hafsan sojan ya taya rundunar murnar nasara da suka yi, da nuna halin dattako da karfin gwiwa, inda ya bukace su da su kara kaimi wajen kai hare-hare a kan masu aikata laifuka a yankin Arewa maso Gabas.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published.