Tsaro

Sojoji sun umarci ‘yan ta’adda da su mika wuya ko kuma su fuskanci ruwan wuta

Spread the love

Rundunar sojin Najeriya ta umarci ragowar ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP da ke ci gaba da kasancewa a maboyarsu da ke yaki da kasar a yankin Arewa maso Gabas da su mika wuya tare da ajiye makamansu kamar yadda mambobinsu da iyalansu sama da 83,000 da suka mika wuya ga sojoji a kasar a Borno ko kuma a fuskanci ruwa wuta na sojoji.

Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa ne ya bayar da wannan umarni a jiya a yayin taron jama’a na sojojin Najeriya na 2022 da aka gudanar a filin Maimalari Cantonment dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Musa ya ce duk da cewa shekarar 2022 na cike da kalubale, amma yankin arewa maso gabas ya samu zaman lafiya da ba a taba ganin irinsa ba ta hanyar gagarumin kokarin da sojoji ke yi na kakkabe ‘yan ta’adda.

Ya kara da cewa yawan ‘yan ta’addan da suka mika wuya ya samo asali ne sakamakon yadda sojoji suka bi wajen aiwatar da yakin.

Bikin na bana wanda ya gudana a Canton Maimalari dake Maiduguri, rundunar Operation Hadin Kai Theater Command da hedikwatar runduna ta 7 ta sojojin Najeriya ta shirya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button