Sojojin Nigeria sunyi nasarar kashe ƴan bindiga 48 tare da cafke wasu daga cikin kwamandojin ƴan ta’addan a Jihar Zamfara.

Rahotannin da suke shigowa yanzu sun tabbatar cewa Jami’an Sojojin Nigeria sun yi nasarar kashe ƴan bindiga 48 yayinda wasu manya-manyan kwamandojin kungiyar ta yan ta’adda suka shiga hannu a Jihar Zamfara.

Mai magana da yawun rundunar Sojoji ta ƙasa Mohammed Yerima shine ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labaru ayau Litinin.

A cewar sa, Jami’an Sojijin sun kuma yi nasarar ceto mutane aƙalla 18 waɗanda ƴan bindigar suka sace a kwanakin baya.

Mista Mohammed Yerima ya ƙara da cewa dakarun sojojin sun yi nasar ƙwato muggan makamai da suka haɗa da bindigu ƙirar AK-47, G3 da tankar yaƙi daga wurin ƴan bindigar.

Har’ilayau wannan gagarumar nasara ta tabbata ne bayan umarnin da Babban Hafson Sojoji na ƙasa COAS Ibrahim Attahiru ya bayar cikin satin da ya gabata.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *