Suna yaki ne da masu adawa da Shugabancin su, ba suna yaki da yan ta’adda bane__Majalisar dinkin duniya ga Shugabannin Najeriya, Chadi, da Nijar.

Tun daga wayewar garin yau Talata majalisar dinkin duniya ta fitar da sakamon binciken da tayi ga shugabannin Afirka ta yamma game da rashin zaman lafiya da ake fama dashi.

MDD ta ce matukar ba a samu sauye sauyen tsarin tafiyar da shugabanci ko kuma samun canjin Shugabannin kasashe guda uku ba, wato Najeriya, Nijar, da Chadi to kawar da rashin tsaro a kasashen nan guda uku abu ne mai wahala.

Majalisar dinkin duniya ta ce rashin zaman lafiyar da Najeriya ke fama dashi, shine ke kara assasa rashin zaman lafiya a Chadi da Nijar.

Majalisar dinkin duniya ta ce ko dai kasar Najeriya ta canza tsarin yadda take tafiyar da Shugabanci ko kuma a samu canjin Shugaba gaba daya, sun yadda da cewa duk Shugabannin kasashen nan guda uku ba da gaske sukeyin yaki da matsalar tsaron yankunan su ba, suna yaki ne kawai da masu Adawa Shugaban cin su ______haka majalisar dinkin duniya ta fada.

Daga Kabiru Ado Muhd.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *