Tsaro
Ta’addanci: ‘Yan Boko Haram Sun kashe Babban Malami a Borno.
A jiya laraba ne mayakan Boko Haram suka kashe mutane 5 cikinsu hadda limamin garin.
Lamarin ya faru ne a garin Banki dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Mayakan sun shiga garin bankin ne da misalin karfe 7 na daren jiya, Inda suka kashe mutane 5 da babban Malamin Garin.
Mayakan Boko Haram din dai suna cigaba da cin karensu ba babbaka a yankin Arewa Maso gabashin kasar.
Sai dai Kungiyar tayi Ikirarin Kafa Sansani a Yankin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso yammacin Kasar Nan.
Ahmed T. Adam Bagas