
An fara yin tonon silili kan yadda Najeriya ta shiga halin da ake ciki na rashin tsaro a kasar.
Abubakar Kawu Baraje, tsohon jigo a jam’iyyar APC mai mulki a ranar Litinin din da ta gabata, ya gano asalin rashin tsaro da ake fama da shi a kasar nan tun bayan kwararowar Fulani daga kasashe makwabta kamar Saliyo, Mali, Senegal, Nijar da Chadi da aka kawo cikin kasar domin zabe a 2015.
Ya bayyana haka ne a garin Ilorin a wani bangare na gudanar da bukukuwan cikar sa shekaru 70 a duniya.
Ya kuma goyi bayan shirin taimakon kai-da-kai na gwamnonin Kudu maso Yamma, inda ya bayyana cewa martanin Sunday Igboho game da rikicin makiyaya ya zama dole domin Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen sauke babban nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da kare rayuka da dukiya.
Dangane da yunkurin da wasu gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki suka yi na neman tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Baraje ya ce jam’iyya mai mulki ta bata lokaci ne kawai.
Baraje, wanda ya taba rike mukamin sakataren jam’iyyar na kasa kuma shugaban jam’iyyar PDP da ta balle, ya ce Fulanin da ke haddasa fitina a kasar nan ba ‘yan asalin Nijeriya ba ne.
“Ba tambayar da ta dace muke yi kan yadda Fulanin da muke zaune da su suka zama wata matsala kwatsam.
“Dole ne mu kuma tambayi yadda suka sami damar yin amfani da bindigogi,” in ji tsohon shugaban jam’iyyar.
Baraje ya ce Fulanin da suke tafka barna a kasar nan ba Fulanin Najeriya ba ne.
“Hukumomin tsaro ba su fito fili ba game da yanayin matsalar.
“Sun yi kama. Me ya sa ba su gaya wa jama’a su wane ne ‘yan ta’addan ba? ya tambaya.
A cewarsa, an kawo Fulanin da ke haddasa matsalolin tsaro a kasar ne domin su taimaka wajen samun nasara a zaben 2015.
“Bayan an yi zabe Fulani sun ki fita. Ni da sauran masu tunani na rubuta kuma muka gargade wadanda muka fara APC da cewa hakan zai faru amma babu wanda ya saurare mu,” ya bayyana.
Madogara: Business Day