Tsaro: Buhari ya sha alwashin fatattakar mugayen ɓatagarin da ke addabar kowani lungu da saƙo na Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abu mai yiwu wa domin ganin ta fatattaki duk wasu bata gari dake ko wani sassan ƙasar nan domin dawo da doka da oda.

Mai bawa shugaban ƙasa shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno ne ya tabbatar da cewa shugaban ya bayyana haka a wani muhimmin taron tsaro da aka yi a Abuja ranar Juma’a nan data gabata.

Monguno ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya kira taron ne ba don komai sai domin a magance matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar wasu sassan ƙasar nan.Ya bayyana cewa taron an ne ɗagesa zuwa ranar talata ta mako mai zuwa, amma har dai har an soma tattaunawa akan muhimman batutuwan da suka shafi tsaron ƙasa.

Ya ce: ‘‘Ya damu da yadda ake ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu sassa na kasar nan, shugaban ƙasar ya kuma kira wani muhimmin taro na majalisar tsaro ta ƙasa a yau, yayin da yake ci gaba da fuskantar halin da ƙasar nan ke ciki gaba gaɗi.

”Bugu da ƙari, a taron na yau, Shugaban ƙasan ya fito ƙarara ya bayyana cewa tunda masu tayar da ƙayar baya, ƴan fashi da masu aikata laifuffuka na ƙara ta’azzara, bazaiyi ƙasa a gwuiwa ba, har sai yaga ansamu nasara. Yayi kuma amanna kan dukkan matsalolin tsaron dake damun mu, tare da ma duk wani abu maras kyau dake tsubure a sassa daban-daban na kasar nan, cewar batare da shakku ba, hukumomin tsaron Najeriya da dukkan mu a matsayin mu na ƙasa ɗaya dunƙulalliya za mu shawo kansu. Yayin da masu aikata laifin ke ci gaba da ƙoƙarin kai gwamnatin Najeriya bango ta hanyar ƙure hakurinmu, tabbas shugaban ƙasa da majalisar zartarwa waɗanda suka ɗage muhimmin taron na yau har zuwa safiyar Talata don karbar ƙarin bayani daga shugabannin tsaro, sun shirya tsaf domin aniyar kawo karshen cin zarafin da ake yi wa al’umma ko ta wani irin hali.

”Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shirye yake tsaf don dauƙar ƙwararan matakai domin amfanin jama’a da kuma ƙasar Najeriya. ‘’Ba za muyi ƙasa a gwuiwa ba har sai an samu zaman lafiya da tsaro sosai a cikin al’ummominmu, kota wani irin hali. “ inji shi.

NAN

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *