Tsaro
TSARO: Gwamna El Rufa’i ya chaccaki APC da Buhari da Gwamnatinsa ta tarayya.


Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi barazanar kawo sojojin haya daga kasashen waje domin yakar ‘yan ta’addan da ke yin katsalandan a dazuzzukan jihar Kaduna idan gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza magance ta’addancin.
Da yake magana da Hausa, El-Rufai ya ce: “Na kai kara ga shugaban kasa, kuma na rantse da Allah, idan ba a dauki mataki ba, mu gwamnoni za mu dauki matakin kare rayukan al’ummarmu.
“Idan yana nufin tura sojojin haya na kasashen waje su zo su yi aikin, za mu yi hakan ne don magance wadannan kalubale.”