Tsohon shugaban kasa Chief Olusegun Obasanjo ya yabawa dakarun sojojin Najeriya na operation lafiya dole reshen jihar borno bisa kokarin da sukai na kwato matan auren da ‘yan boko haram suka kwashe a harin zabarmari ta jihar Borno.

Tsohon shugaban kasa Chief Olusegun Obasanjo ya yabawa dakarun sojojin Najeriya na operation lafiya dole reshen jihar borno bisa kokarin da sukai na kwato matan auren da ‘yan boko haram suka kwashe a harin zabarmari ta jihar Borno.

Obasanjo yace ba karamin kokari dakarun sojojin Najeriya sukai ba wajen kwato matan auren duba da irin dabarun yakin da sukai amfani dasu cikin sirri ba tare da fargaba ko nuna tsoro ba.

Chief Olusegun Obasanjo ya kara da cewa yana kira ga rundunar sojan Najeriya data cigaba da zakulo dabarun yaki irin wanda dakarun sojojin Najeriya na operation lafiya dole sukai amfani dashi wajen kwato matan auren da ko sati guda ba ayi da sace su ba bayan an yiwa matasan kauyen kisan yankan rago.

Obasanjo yace hakama yana dada shawartar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da ya jinjinawa dakarun sojojin Najeriya ta operation lafiya dole bisa wannan sababbin dabarun yakin da suka bijiro dashi har sukai Nasara a Dan kankanin lokacin da ‘yan kasa basuyi zato ba.

Sannan yace ya kamata shugaban kasar ya dada tilastawa dakarun sojojin Najeriya gaba daya cewa ya zama dole suci gaba da bijiro da sabbin dabarun yaki domin a tabbatar an samu nasarar kawar da ‘yan ta’addan da suka addabi kasar baki daya.

Fassara Daga Kabiru Ado Muhd.

Leave a Reply

Your email address will not be published.