Tsaro

Tun daren jiya alhamis ‘yan bindiga suke ta barin wuta a wasu yankuna na karamar hukumar Giwa dake Jahar Kaduna har zuwa safiyar yau Jum’a.

Spread the love

Tun daren jiya alhamis ‘yan bindiga suke ta barin wuta a wasu yankuna na karamar hukumar Giwa dake Jahar Kaduna har zuwa safiyar yau Jum’at.

Mun tattauna da wani Wanda abun ya shafa, ya tabbatar mana da cewa har yanzun Allah ne kawai yasan yawan mutanen da aka kashe da kuma yawan mutanen da aka kwashe zuwa daji.

Kauyukan da abun ya shafa sune:
=Dillalai.
=Bare-Bari.
=Unguwar Bakko.
=Zangon Tama.

Wani abun takaici shine, ‘Yan ta’addan sun hana yiwa mutanen da suka kashe sallar janaza.

Yanzun haka mutanen kauyukan sun fara kwararowa cikin garin Giwa don samun mafaka.

Daga:Sunusi (D) Danmaliki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button