Yadda Ƴan sanda suka cika hannu dumu-dumu da wani ɗan sandan bogi.

A ranar Alhamis da karfe 9 na safe ne rundunar ƴan sanda ta jihar Legas, reshen Orile ta kama wani magidanci mai suna Augustine ɗan shekara 39, kan titin Ishola, Magogo a Yaba, a Orile Bus Stop.

ƴan sandan sun tsayar da babur ɗin wanda ake zargine, yayin da ya gabatar da kansa a matsayin dan sanda shima.

Bayan da ƴan sandan gaskiyan suka matsa masa da tambayoyi ne, sai suka fahimci da walakin goro a miya sakamakon ganewa da suka yi cewar mutumin baya da gamsarsun amsoshi masu korar da shakka daga zato.

Daga nan ne sai sukayi caraf dashi, inda suka same shi tare da katin izinin zama ɗan ‘yan sanda amma katin bogi.

Ai kuwa nan da nan, ƴan sanda sukace dawa aka haɗamu idan bada kai ba, sakamakon haka ne yasa aka tasa ƙeyar Augustine gidansa, inda acan ɗin ma aka samu rigar ƴan sanda guda ɗaya, hula hana salla ɗaya itama, da kuma wasu kayayyaki da ƴan sanda ke amfani dasu.

Bugu da ƙari, jami’an ‘yan sanda da ke sashin Itire suma sun samu nasarar kama wani mai suna Samuel Ayooluwa, mai shekaru 24, a gida mai lamba 54, kan titin Olatilewa na Lawanson a Surulere, Legas.

Jami’an, yayin da suke ci gaba da sintiri a yankin, sun amsa kiran matsi daga ɗaya daga cikin masu shagunan a adireshin.

Mai wayar ya ce wasu mutane uku ɗauke da makamai a kan babur sun far wa kwastomomin da ke cikin shagon sannan suka ƙwace musu kayayyakinsu.

Bayan anbi sawun maharanne kuma, aka kame Samuel; yayin da sauran suka tsere.

An samu ƙaramar bindiga ƙirar gida, mai ɗauke da harsasai masu rai uku, harsasai uku da aka kashe da kuma wayoyin hannu biyu.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Lagos, Hakeem Odumosu ya ba da umarnin a tura waɗanda ake zargin zuwa sashin ƴan sanda na musamman don gudanar da bincike.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *