Yadda akayi shahararren mai Garkuwa Da Mutane “Yellow Dan Mangoro” ya shiga hannun ƴan sanda dumu dumu bayan yaƙi jin nasihar Dr Ahmad Gumi.

Yellow ɗan Mongoro a daji

Shi dai Abubakar Ali shine shugaban ƴan ta’addan da suke garkuwa da mutane waɗanda suka bi suka addabi jihar Niger.

Ana masa laƙabi da Yellow Dan Mangoro ne saboda mutum ne fari fat, to amma kamar yadda tarihin rayuwar sa take, zuciyar Yellow Dan Mangoro baƙa ƙirin take kamar gawayi.

Watanni biyu da suka shuɗe idan za’a iya tunawa, Sheikh Dr Ahmad Gumi (H) yayi ta maza yakai ziyarar neman sabunta tunanin ƴan ta’addan har can cikin jeji inda suke cin karen su babu babbaka, har ya haɗu da wannan shugaban nasu mai suna Yellow Dan Mangoro.

Dr. Ahmad Gumi cikin ikon Allah a wancan lokacin yayi musu nasiha akan su ajiye makamai su dena ta’addancin, amma bai ji nasihar ba.

Zaratan jami’an tsaron kasar Najeriya na ƴan sanda, sun ɗana masa wani ƙatoton tarko daga gefe, cikin salon nan na farauta.

Cikin ikon Allah, ya saki jiki yanata ɗiban sharholiyar sa, ai kuwa jikake rammm, ƴan sandan sun kamashi tare da wasu yaransa, kuma an samu bindigogi da harsashi masu yawa a tare da shi.

Farko bayan an kamashi

Lokacin yana jeji a ranar da suka hadu da Dr Ahmad Gumi

Allah ka shiga tsakanin nagari da mugu.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *