Yadda Wasu Matasa Suka ƙona Helkwatar Ƴan Sanda Da Wani Dan Bindiga a Jihar Sokoto

Kudu, Arewa, da Tsakiyar Najeriya a ƴan kwanakin nan suna cikin tashin hankali, a saboda haka ne, yanayin tsaro a ɓangarorin ya koma ɗaukar sabon salo, ta yadda zaka ga jama’a yanzu sun soma ɗaukar wa kansu hukunci batare da sun bari jami’an tsaro waɗanda alhakin yin hakan ke kansu ba, sunzo sun ɗauka.

A irin waɗannan ɗaukar wa kai hukunci ne, yasa wani abu mai rikitarwa ya faru a garin Sokoto.

Da sanyin safiyar talata ne, wasu da ake tunanin ƴan bindiga ne suka shiga cikin kauyen Kainuwa, ƙaramar hukumar Kwari dake Jihar Sokoto.

Koda shigar su, suka far wa mutane, har sukayi wa wani mutum Alhaji fashi.

Koda suka bar garin domin gudun kar a kamasu, sai jama’ar garin cikin ƙarfin hali suka bar gidajensu suka bi waɗannan yan fashin suma.

Ai kuwa cikin ikon Allah, sai suka tarar da wasu mutane har su shida, nan da nan sukace dawa aka haɗamu idan bada ku ba, caraf suka kama su aka cewa sune barayin nan.

Kamar yadda ya dace, sai mutanen nan suka damƙa su a hannun jami’an tsaro, domin ɗaukar matakan da suka kamata, a inda rundunar ‘yan sanda ta hannun DPO ɗin yankin suka amshi barayin, sai jama’ar suka nemi da lallai sai an kashe mutanen nan hankalin su zai kwanta, kamar yadda kakakin yan sandan na jihar Sokoto ASP Sanusi Abubakar ya tabbatar.

A cewar mutanen, dole ne a kashe su tunda suna kashe mutane, to amma hukumar yan sanda sun dage akan cewa, dole ne sai anyi bincike sannan za’a tabbatar da ko yan fashi ne ko akasin haka.

Saboda an hana su ne, mutanen suka harzuka har sukayi ƙoƙarin ƙwatarsu, wanda sanadiyyar haka ne yasa mutanen suka kona motar mutanen da kuma wasu motoci na ƴan sanda dake kewayen wajen.

Wannan sa-to-ka-sa-katsin data faru sai data kai ga mutum ɗaya ya rasa rayuwarsa, bayaga cinna wa ofishin ƴan sandan wuta da fusatattun mutanen sukayi.

To amma ASP Sanusi Abubakar ya tabbatar da cewa yanzu haka an kama wasu daga cikin waɗanda sukayi wannan aika aikan, kuma zasu ci gaba da kokarin kama ragowar, tunda duk sun san su.

Wannan na zuwa ne lokacin da wasu al’ummomi ke ta fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda musamman a gabascin Sakkwato duk da watan azumi da ake ciki.

Bisa ga yadda jama’a ke kokawa akan ayukkan ta’addanci da ke salwantar da rayukan da dukiyoyi, rashin samar da hanyoyin magance wannan matsalar kan iya haifar da wasu matsaloli a nan gaba kamar yadda alamu suka nuna na jama’a na son a bari su kashe yan ta’adda da kan su.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *