Tsaro

‘Yan bindiga sun kashe mutane 37 a Kaduna, sun kona gidaje

Spread the love

Akalla mutane 37 ne rahotanni suka ce ‘yan bindiga sun kashe a wasu sabbin hare-hare a karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.

Hare-haren sun auku ne daban-daban a daren Lahadi a kauyukan Malagum 1 da Sokwong na masarautar Kagoro a karamar hukumar Kaura ta jihar.

Duk da cewa hukumar ‘yan sanda ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba, Kakakin Majalisar Dokokin Karamar Hukumar Kaura, Shugaban Karamar Hukumar Kauru, Hon Atuk Stephen, ya shaida wa gidan Talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne a daidai lokacin da misalin karfe 11 na daren ranar Lahadi inda suka kai harin da ya kashe mutane 37.

Ya kuma ce ‘yan bindigar sun kona gidaje sama da 100 tare da lalata motoci da babura da dama a yayin harin.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun lalata dukkan gidaje a yankin Sokwong gaba daya, yayin da yankin ya zama ba kowa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button