Tsaro

‘Yan bindiga sun kashe mutane Ashirin da tara 29 a jihar Kaduna

Spread the love

‘Yan bindigar, wadanda suka kai hari a cikin al’ummomin ranar Lahadi da daddare, sun kuma kona gidaje da dama.

Al’ummomin da abin ya shafa sun hada da Malagum 1 da Sokwong na Kagoro, a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.

Da yake tabbatar da kashe-kashen, shugaban karamar hukumar, Mista Mathias Siman, ya ce an kashe mutane bakwai a yankin Sokwong kuma an kone su gaba daya.

Haka kuma, Kakakin Kaura LG, Mista Atuk Stephen, ya ce an kashe sama da mutane 22 a yankin Malagum 1.

Da take mayar da martani, kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kaduna, CAN, ta ce tana alhinin mutuwar sama da mutane 28 da ba su ji ba ba su gani ba, na al’ummar Mallagum da ke yankin Kagoro da aka yi wa kisan gilla a daren Lahadi.

Shugaban kungiyar CAN a jihar, Rabaran John Joseph Hayab, ya ce “Wannan kisan kiyashi ya kara tabbatar da cewa har yanzu ba a kawar da wadanda suka kashe mutanen Kudancin Kaduna ba kamar yadda ake ikirari.

“Gwamnatin tarayya da jami’an tsaro kar su bar masu kisan su tsere. Wadanda suka aikata wannan aika-aika dole ne a kamo su a hukunta su.

“Wadannan sabbin kashe-kashen na iya zama wata dabarar tsoratar da jama’a daga yin amfani da ‘yancinsu da kuma kara fargaba da talauta su.

“Haka zalika kungiyar ta CAN ta yi Allah-wadai da wannan ta’asa da kakkausar murya, amma ta yi kira da a kwantar da hankula, inda ta yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyi.”

A nata bangaren, gwamnatin jihar Kaduna ta mika sakon ta’aziyya ga al’ummar Malagum da Sokwong dake karamar hukumar Kaura.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya ce “Sojoji da sauran jami’an tsaro sun ruwaito cewa ‘yan bindiga sun kai hari a wuraren tare da kashe ‘yan kasa da dama tare da kona gidaje da sauran kadarori.

“Gwamna Nasir el-Rufai ya bayyana matukar bakin cikinsa da rahoton faruwar lamarin, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda aka kashe, yayin da yake jajantawa iyalansu. Gwamnan ya yi Allah-wadai da hare-haren a matsayin rashin bin doka, duba da kokarin gwamnati, jami’an tsaro, da cibiyar gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a cikin mako guda da ya gabata.

“Gwamnan ya kuma umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar, SEMA, da ta samar da kayan agaji ga al’umma cikin gaggawa.

“Hedikwatar tsaro na Operation Safe Haven na gudanar da aikin tsaro cikin gaggawa, domin a halin yanzu Kwamandan wanda shi ne GOC 3 Division na Sojojin Najeriya, Manjo Janar Ibrahim Ali, da Kwamandan Sashe na 7, Kanar Timothy Opurum suna nan a wurin.

“Gwamnatin jihar Kaduna za ta yi karin bayani kan lamarin yayin da take samun martani daga jami’an tsaro.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button