‘Yan Bindiga sun sace Hakimi a Jihar Adamawa.

Wasu ‘yan bindiga sun sace hakimin MaFarang da ke karamar hukumar Mayobelwa a jihar Adamawa, Ardo Mustapha Ardo Ahmadu.

An sace Hakimin, wanda kuma ke rike da sarautar Sarkin Noman Adamawa, ‘yan awanni bayan dawowarsa daga Abuja.

Mazauna gari sun ruwaito cewa wasu mutane dauke da makamai sun dauke shi daga gidansa da misalin karfe 12 na daren jiya Litinin bayan sun ci karfin ’yan banga da ke kokarin yin turjiya kan tafiya da basaraken.

Wani shaidar gani da ido, wanda baya son a bayyana sunansa, ya ce maharan, wadanda ke dauke da manyan makamai, sun yi ta harbe-harbe babu kakkautawa, lamarin da ya tilasta wa ’yan banga na yankin komawa baya.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar ta Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rundunar ta tura jami’anta domin su ceto basaraken.

Nguroje yace “gaskiya ne an sace basaraken tsakanin 12 na dare zuwa 1:00 na dare”, in ji shi.

“Yanzu haka muna kan gudanar da Aiki tukuru domin ceto shi, da kuma kama ‘yan Bindigar ba tare da sun Illata shi ba. Inji Shi.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *