Tsaro

‘Yan bindiga sun sace matar dan majalisa da ‘ya’yansa a Zamfara

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mata da ‘ya’ya hudu, da kuma makwabta biyu na dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Aminu Ardo Jangebe.

An kai harin ne a garin Jangebe da ke karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara, kuma dan majalisar baya gida lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari.

An kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu makusantan sa biyu, Alhaji Yahaya da Sa’adu Mainama.

Wani mazaunin unguwar, Sani Abubakar, da yake zantawa da manema labarai ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun isa garin ne da misalin karfe 11 na daren ranar Alhamis inda suka fara harbe-harbe ba da dadewa ba don tsoratar da mutane.

Jama’a da dama sun gudu da jin karar harbe-harbe a cewar Abubakar, yayin da wasu kuma suka rufe kofarsu don gudun kada a sace su.

Ya yi ikirarin cewa ‘yan bindigar sun je gidan Aminu Ardo ne suka fasa kofar don shiga.

Ya ce, “Nan take ‘yan fashin suka shiga gidan, suka yi awon gaba da matar Honourable da ‘ya’yansa hudu.

“A lokacin da suke fitowa daga gidan, sai suka hango wasu makwabtansa guda biyu, MalamYahaya da Sa,adu Mainama wadanda suma suka yi awon gaba da su.”

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu kan lamarin, ya ce “har yanzu ban samu cikakken bayani ba”.

Sai dai har yanzu bai bayar da cikakken bayani ba har zuwa lokacin gabatar da rahoton.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button