‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Miyetti Allah A Jahar Kogi

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) a jihar Kogi, Wakili Damina.

A cewar sakataren kungiyar ta MACBAN, Adamu Abubakar, wasu mutane dauke da makamai sanye da kayan sojoji ne suka sace Damina a ranar talatin ga Afrilu.

Ya lura cewa shaidu sun ce masu garkuwar, wadanda yawansu ya kai takwas, sun zo ne a wata farar bas da misalin karfe sha biyu na rana don su dauke shugaban daga cikin gidansa da karfi a kauyen Chikara, da ke Karamar Hukumar Kogi.

Abubakar ya ce kanin Damina ne ya sanar da shi faruwar lamarin bayan awa daya, wanda ya ce ya ga abin da ya faru.

Sakataren ya ce nan take ya kira lambar wayar shugaban da ya bata, amma bai samu wayar ba.

Ya ce wayar Damina na kashe lokacin da ya buga waya bayan awa daya.

“Tun daga wannan lokacin, layukan nasa ba su kai labari ba kuma duk kokarin sanin inda yake ya ci tura,” in ji shi.

Ya ce shi da wasu mambobin kungiyar sun ziyarci hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta Najeriya, Abuja, don sanin ko Damina yana hannunsu amma suka ce a’a.

Ya ce kungiyar bincike da MACBAN ta kafa sun ziyarci wasu wurare, ciki har da mayanka dabbobi a ciki da wajen Abuja amma ba a samu nasara ba.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Ede Ayuba, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce har yanzu ‘yan sanda ba su gano inda shugaban ya ke ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *