Yan bindiga sun sake afkawa Neja, sun kori al’ummomi 8

Akalla kauyuka takwas da suka kunshi kimanin mazauna 1,500 ne ‘yan bindiga suka kora daga karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

An tattaro cewa yan fashin wadanda yawansu yakai 60, a yammacin ranar Asabar, sun mamaye yankin Fuka akan babura dauke da bindigogin AK-47.

Majiyoyi sun ce lokacin da suka isa kauyen Fuka, ‘yan fashin sun nufa kai tsaye ga wani shahararren dan kasuwa, Alhaji Doma Fuka, inda daga nan aka ce sun wuce zuwa gidan wani dan majalisar dokokin Jihar Neja, Mista Andrew Doma.

An tattaro ‘yan fashin, bayan tilastawa mazauna kauyukan daga gidajensu sun bi gida-gida suna satar kudi da wasu kayayyaki masu amfani tare da sace shanun su.

Da yawa daga cikin mazauna kauyukan galibi mata da yara ‘yan ta’addan sun ji musu raunuka kuma nan take aka garzaya da su zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba.

Yanzu haka ‘yan kungiyar sa-kai a cikin al’ummomin da abin ya shafa suna ci gaba da farautar’ yan ta’addan don kamo su da kuma kwato shanun su.

Da yake karin haske game da lamarin, wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa ba a iya tantance adadin wadanda aka sace ba.

“Ban tabbatar da adadin wadanda aka kashe ko wadanda aka sace ba amma zan iya tabbatar muku da cewa babu kowa a cikin wadannan al’ummomin yanzu saboda ‘yan bindigar sun mayar da kauyukan wuraren da suke buya da wuraren girkinsu,” in ji shi.

Kokarin jin ta bakin ‘yan sanda ya ci tura saboda ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar‘ yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ba.

Kodayake, wani ma’aikacin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja a cikin Sarkin Pawaa, ya tabbatar da labarin.

0 thoughts on “Yan bindiga sun sake afkawa Neja, sun kori al’ummomi 8

  • April 26, 2021 at 11:07 am
    Permalink

    Allah ya kawo musu agaji

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *