Yan bindiga sun sake bankawa ofishin ƴan Sanda wuta a Jihar Akwa-Ibom.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan bindiga sun sake kai harin ta’addanci a wani ofishin ƴan Sanda a Jihar Akwa-Ibom dake kudu maso kudancin Nigeria.

Awanni 24 da suke wuce ne dai aka tabbatar da kisan aƙalla jami’an ƴan Sanda biyar tare da uwar-ɗakin ɗaya daga cikin jami’an ƴan sandan a wani hari da ƴan bindiga suka kai a Jihar ta Akwa-Ibom.

Wani jami’in ɗan Sanda wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa shine ya tabbatar da faruwar al’amarin cikin maraicen wannan rana ta Lahadi a ƙaramar hukumar Abak dake Jihar Akwa-Ibom.

Ɗan sandan ya sake tabbatar da cewa babu asarar rai, amma ababen hawa da dama sun ƙone ƙurmus sakamakon harin.

Har’ilayau, aƙalla ofisoshin ƴan Sanda biyar aka kaiwa hari kwana-kwanan nan cikin ƙananan hukumomin da suka haɗa da – Essien Udim, Ika, Ini, Ikono da kuma Abak duk a Jihar ta Akwa-Ibom.

Ana dai ganin yadda ƴan ta’adda suke cigaba da kaiwa Jami’an tsaro hari a yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudancin Nigeria. Ko wanne mataki gwamnati take yunƙurin ɗauka domin daƙile wannan matsaloli?

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *