Tsaro

‘Yan bindiga sun yi Garkuwa da mutun ashirin 20 a hanyar Kaduna Abuja bayan sa’o’i 22 da Sefeton ‘yan Sandan nageriya IGP Alkali ya Kai ziyara sintiri.

Spread the love

Daruruwan ‘yan bindiga ne suka kai farmaki wasu gidaje a Anguwar Maji da ke cikin garin Jere a jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da wasu mutane 22 a ranar Lahadi.

An tattaro Rahoton ne ne sa’o’i 24 bayan babban sufeton ‘yan sanda na kasa (IGP), Baba Usman Alkali ya je sintiri a babbar hanyar Abuja/Kaduna mai cike da cunkoso.

Sufeto Janar na ‘yan sandan da ke sintiri a ranar Lahadi, ya shaida wa manema labarai cewa, hanyar ba ta da hadari ga jama’a a yanxu

Sai dai wani mazaunin Anguwar Maji mai suna Shehu Bala, ya ce sabuwar garkuwar ta faru ne da misalin karfe 11 na daren ranar Lahadi lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye al’ummar garin.

Ya ce maharan da suka zo da yawa sun mamaye gidaje da dama tare da yin awon gaba da mutanen kauyen 22 da suka hada da mata biyar.

“’Yan bindigar sun zo da adadi mai yawa yayin da wasunsu ke sanye da kakin sojoji.

Suna tafiya gida gida suna tada wadanda abin ya shafa kafin su kai su daji da bindiga.”

Bala ya ce daya daga cikin mutane 22 da aka yi garkuwa da su ya tsere daga hannun wadanda suka sace shi yayin da ake kai su cikin daji.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a iya samun ‘yan sanda don tabbatar da hakan ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button