A jiya Asabar ne Kungiyar, Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād da Akafi Sani da (Boko Haram) suka fitar da wani bidiyo da ke nuna tankar yaki, harsashi da dubunnan alburusai da kungiyar ta ta’addancin ta ce ta kwace a dajin Sambisa, da ke jihar Borno.
Wani dan kungiyar ya bayyana a cikin faifan bidiyo na minti 4.da dakika15 yana magana a kan artabun da aka yi tsakanin maharan da Sojojin Najeriya a cikin dajin Sambisa da ake fargabar Shiga.
Mayakan kungiyar sun nuna wata tankar yaki ta Vickers Mk.3 Eagle, sama da harsasai guda goma da kuma dubunnan harsasai.
Bidiyon shi ne alama ta farko da ke nuna cewa sojojin Najeriyar na yin wani samame kan kungiyar Boko Haram da Abubakar Shekau ke jagoranta a Sambisa, cibiyar matattarar ‘yan tawaye a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da dakarun Soji ta ‘Operation Tura Takai Bango’ da aka kaddamar kwanan nan ke niyya ganin bayan ISWAP da Boko Haram, a dajin Alagarno – yankin triangle na Timbuktu, da Sambisa.
Tun daga shekarar 2009, kungiyar Boko Haram da reshenta na kungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) suka tsunduma cikin wani yakin Ta’addanci, wanda ya kai ga rasa rayukan mutane sama da 30,000 da kuma raba mutane miliyan 2.5 da muhallansu a Kasar Nan.
Ahmed T. Adam Bagas ✍️