‘Yan Boko Haram sun yi harbe-harbe da tashin bama-bamai a Maiduguri.

Harbe harbe da tashin bama bamai da ‘yan kungiyar boko haram suka rikayi ya mamaye wasu sassa Na babban birnin jihar Borno inda yayi sanadiyar rasa rayukan mutane da dama, tare da jikkata wasu da dama.

Kuma ‘yan haramtacciyar kungiyar ta boko haram sun rika harba rokoki da gurneti tun misalin karfe 7:00 daidai Na yammacin yau Talata.

‘Yan boko haram din sunfara kaddamar da hare haren nasu ta kusa da Kaleri dake bayan jami’ar Maiduguri, Adam kolo, Limanti, da Kagarmari dake cikin garin Borno.

Sannan sun ci gaba da fadada hare haren nasu har Fori da kuma Babbar Gonar Cashew kusa da barikin sojojin jihar Borno.

Sannan ‘yan boko haram din sunyita kokarin kutsa kai cikin garin Borno adaidai lokacin sojojin Najeriya suka kawo dauki.

Daga kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *