‘Yan fashi da masu garkuwa da mutane suna addabar jihar Kaduna ne saboda mun ki mu basu kudi mu tattauna da su – in ji Gwamna El-Rufa’i.

Gwamnan jihar Kaduna malam Nasir El-Rufa’i ya ce ‘Yan fashi da masu satar mutane suna addabar jihar Kaduna saboda sun ki ba su kudi su tattauna da su. Gwman Nasir El-Rufai ya fadi hakan ne yayin da ake hira da shi a cukin shirin Sunday Politics na gidan Talabijin na Channel.

Da yake magana akan batun daliban kwalejin da suke hannu ‘yan ta’adda kuwa cewa yayi “Za a dauki matakin dole … da yardar Allah, za mu kubutar da su”.

Gwamnan ya kara da cewa “Babu wata al’umma mai wayewa da zata zauna lokacin da aka kalubalanci yancinta … abu na farko da za ayi shine kawar da wadannan ‘yan ta’addan. Wannan yaƙi ne. Dole ne mu yaƙe su har zuwa ƙarshe”.

Ya kara da cewa “Sojojin Najeriya da hukumomin tsaro, a matsayin matakin gaggawa, na bukatar mallakar manyan makamai don yaki da rashin tsaro. Maganin matsalar tsaronmu ita ce ‘yan sandan jihohi kuma muna aiki a kan haka”. In ji Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *