Tsaro

‘Yan ta’adda dauke da makamai sun mamaye tashar jirgin kasa inda suka yi awon gaba da fasinjoji da dama

Spread the love

‘Yan ta’adda dauke da AK47 sun kai hari tashar jirgin kasa ta Igueben a daidai lokacin da fasinjoji ke jiran shiga jirgin.

A jiya ne wasu dauke da makamai suka mamaye tashar jirgin kasa ta Igueben da ke jihar Edo inda suka yi awon gaba da fasinjoji da dama tare da jikkata wasu da dama.

Kawo yanzu dai ba a sami rahoton mutuwa a lamarin ba.

A cewar wata sanarwa da hukumomin ‘yan sandan suka fitar, mutanen dauke da bindigogi kirar AK47 sun kai farmaki tashar ne a lokacin da fasinjoji ke dakon shiga jirgin, inda suka rika harbin iska da kuma fasinjojin, lamarin da ya sa wadanda lamarin ya rutsa da su suka samu munanan raunukan harbin bindiga.

“Muna sanar da ‘yan jarida cewa a yau 7 ga Janairu, 2023 da misalin karfe 16:00, wasu ‘yan bindiga da ba a tantance adadinsu ba dauke da bindigogi kirar AK 47 sun kai hari tashar jirgin kasa da ke Igueben jihar Edo tare da yin garkuwa da fasinjojin da ba a tantance adadinsu ba, wadanda za su hau jirgin zuwa Warri.

“Masu garkuwa da mutanen da suka yi harbin iska kafin sun yi garkuwa da wasu fasinjojin sun bar wasu mutane da raunukan harsashi.

“Kwamandan yankin Irrua, DPO Igueben Division, da dakarunsa sun ziyarci wurin da lamarin ya faru tare da jami’an tsaro na jihar Edo, ‘yan banga, da mafarauta da nufin kare rayuka da dukiyoyin sauran fasinjojin,” Chidi Nwabuzor. Kakakin ‘yan sanda a jihar Edo ya rubuta.

Peoples Gazette

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button