‘Yan Ta’adda Sun Kashe Manoma 7, a Jihar Neja.

Wasu ‘Yan Bindiga Sun bude wuta kan wasu manoma da suka dauko amfanin Gonarsu daga Gona zuwa gida.

Wannan lamari ya Farune a kauyen Babban Rami dake Karamar Hukumar Mashegu dake Jihar Neja.

Jihar neja na fama da Ta’addacin masu garkuwa sa mutane.

Ko a kwanakin Baya sun Sace Sarkin Madaka dake karamar Hukumar Shiroro a Jihar kuma Suka Kashe shi.

Yanzu haka Sarkin garin Yakila dake Karamar Hukumar Rafi ta Jihar, yana Tsare Hannun Masu garkuwa da Mutane, Inda suka Nemi kudin Fansa Miliyan 15m. Sai dai ankai Miliyan 4m. Amma basu Sakeshi ba.

Jihar Neja na Fama da Matsalar Tsaro Matuka.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *