‘Yan Ta’addan Alka’ida Sun Fara Shiga Jihohin Arewa Maso Yammacin Najeriya__kasar Amurka Ta Ankarar Da Buhari.

Daga Kabiru Ado Muhd

Gwamnatin kasar Amurka ta bayyanawa duniya cewa mambobin kungiyar ‘yan ta’addan Alqa’ida sun fara ratsawa jihohin Arewa maso yammacin Najeriya.

Kwamandan sojojin Amurka Na harkoki Na musamman a nahiyar Africa daga Anderson, Wanda ya bayyana hakan yayin hira da manema Labarai,

Ya ce kungiyar Na shiga wurare daban daban a nahiyar Africa.

A jawabin da the cable ta samu daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka Anderson yace Amurka zata ci gaba da hadakai da Najeriya wajen raba bayanan binciken sirri.

Jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sune Kaduna, kano, katsina, jigawa, zamfara kebbi da sokoto.

Anderson yace sun gano cewa mutane ne masu taurin Kai, kuma duk da kanana ne, kuma suna amfani da kafafen sada zumunta wajen daukan sabbin mambobi kuma suna samu.

Anderson yace abinda zaisa kokarin kasashen duniya ya haifi da me ido shine idan gwamnatin Nigeria tayi hobbasa wajen gudanar da yaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published.