Yan’Bindiga Sun toshe hanyar Zungeru zuwa Tegina dai-dai da gadar Zungeru wurin yan’kifi.

A jiya ne yan bindiga suka kai hari yankin zungeru a Jihar Neja

Wani rahoton da muka samu shine cewa Yan’Bindigan sun kwashe sama da sa’o’i uku suna cin Karen su babu babbaka.

Inda Motoci Suka tsaya daga dukkanin bangarorin titin, Kuma ance Yan’Bindigan sun Koro shanu ne daga cikin daji kusan su dari biyu rike da manyan Makamai.

Duk da cewa akwai sojoji a kusa da wurin, Amma Wani Wanda Ke wurin ya shaida cewa Babu Wani Yunkurin tunkarar barayin.

Daga: Maryam Ango

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *